Saturday, October 20, 2018

[LABARAI] Kotu Ta Bada Umarnin Dakatar Da Gasar Wasan Polo Da Ake Gudanarwa A Kaduna

Babbar kotun daukaka kara ta Jihar kaduna,ta bada umarni cikin gaggawa ga masu shirya gasar wasan Polo ta kaduna da cewar su dakatar da wannan gasa nan take ba tare da wani bata lokaci ba.
Bayanin Haka na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa Wacce ta samu sanya hannun Sakataren Kungiyar na kasa baki daya, Alhaji Mohammad Baba Kyari sannan aka rarrabata ga manema labarai a kaduna a ranar juma’ar nan, ya bayyana cewar tuni umarnin kotun ya kai ga Shugaban Kungiyar Polo ta Jihar kaduna Alhaji Suleman Abubakar.
Sakataren Kungiyar ya kara da cewar, yana sanar da Jama’a cewar da akwai kwakkwaran mataki na Shari’a da zai yi aiki akan Alhaji Suleman Abubakar muddin yayi wani yunkuri na bijirewa umarnin Kotun.
Kwamitin amintattu na Kungiyar Polo ta Kasa suka shigar da kara a gaban Kotun ta kaduna, suna bukatar a dakatar da cigaba da gudanar da gasar ta Kaduna, Sakamakon wata rashin jituwa da ta shiga tsakanin su da Shugaban Kungiyar Polo ta Jihar kaduna Alhaji Suleman Abubakar.
#Rariya

No comments:

Post a Comment