Wednesday, April 4, 2018

[SIYASA] TSOHON DAN WASAN SUPER EAGLE KANU ZAI TSAYA TAKARAR SHUGABAN KASA A 2019



ZABEN 2019: Fitaccen dan wasan kwallon kafa Kanu Nwankwo, ya
bayyana cewar zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2019 dake
tafe.

Kanu yasha alwashin cewar, zai kawo Karshen mulkin shugaban kasa
Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Kanu ya kara da cewar shekaru
18 da suka shude babu abunda gwamnatoti sukayi banda jefa yan
Najeriya cikin halin kunci da rashin tsaro.

Kanu yayi wannan kalami ne a lokacin da yake hira da kamfanin
jaridar wasanni ta Goal.com .

Shafin jaridar Daily post, ta nakalto
Kanu na cewar "Nasarar da George Weah yasamu a zaben kasar
Liberia, yar manuniya ce ga tabbatuwar mafarki na idan har yan
Najeriya suka mara min baya.

Sai dai Kanu bai bayyana jam'iyar da zai tsaya takara cikin ta ba.

Daga Haji Shehu

No comments:

Post a Comment