Monday, April 2, 2018

[LABARAI] MAYAKAN BOKO HARAM SUN KASHE MUTUM 18 A WANI HARI DA SUKA KAI MAIDUGURI
Rahotanni sun tabbatar da cewa mayakan Boko haram sun kai wasu
sabbin hare hare a kauyakun Bale Shuwa da Bale Kura da ke gefen
garin Maiduguri inda suka kashe akalla mutane 18.
Wadanda al'amarin ya auku a kan idonsu sun bayyana cewa mayakan
Boko Haram din sun kuma raunana akalla mutane 55 a yayin harin.
Sai dai har yanzu gwamnati ba ta ce uffan ba a kan hare haren.

Daga Rariya

No comments:

Post a Comment