Wednesday, February 7, 2018

[KANNYWOOD] GABAR ALI NUHU DA ADAM A ZAGO: ME YASA YARAN ALI NUHU SUKA YIWA BMB ZAGIN KARE DANGI?


Tun a farkon shekarar nan ake takun saka tsakanin Ali
Nuhu da Adam A Zango, amma dalilin wannan Gaba shine
har yanzu ba'a Gama sani ba. Sai dai akwai zargi daga
dukkan bangarorin inda bangaren Zango suke cewa Ali
Nuhu yana bakin ciki da cigaban da Adamun yake samu,
yayin da su kuma banagaren Alin suke cewa na kusa da
Adamun sune suke zuga shi domin ganin sun shiga tsakanin
Adamun da Ali.

 Zargin da kowa ne bangare yasha
musantawa.
Abun ya fara fitowa fili ne bayan da Adam A zango ya saki
fim dinsa mai suna Gwaska Return a Ado Bayero cinema
inda wasu Jarumai maza da mata suka je amma ba'a ga
keyar Ali Nuhun ba ko kuma wani na kusa dashi.

Abun ya qara zafi ne bayan yaran Ali Nuhu sun yi ma Bello
Muhammad Bello zagin qare dangi bisa zargin cewa yana
habaici akan Ali Nuhu sannan yana zuga Adam Zango.

Tunda ake wannan maganganu ba wanda yace komai
tsakanin Ali da Adamu, bayan faruwar dukkan wadan
abubuwa Adamun ya fito yayi magana inda yace shifa
rikicin sa ba da Ali Nuhu bane, inda daga bisani kuma yayi
wani dogon rubutu kamar haka

" B A U T A K O Z A L I N C I

A Yau wasu daga cikin Jarumai MAZA da MATA tsofaffi
da manya da kananan da wani bangare na Maaikata a
kannywood. Suka kai kara da kukan wasu manyan
producers da kananan su.! Gurin Hukumar tace fina-finai.

Kan abin da suke kira danne hakki da mugunta da producers
din suke musu.

A cewarsu mafi yawan ayyukan da suke da producers din
basa biyansu ko kuma in zaa biya ka a baka kudin da ko na
mota bazai kai ba.

 Ko ayi kwanaki ana aiki da kai, in an
gama ace za'a kiraka, shikenan an cinye.

Tabbas duk abin
da mutum sama da Ashirin Mata da maza suka fada, to
lallai yana faruwa. Kuma hakan zalincine
Allah bazai kyaleba..

 Yaku masu wannan dabiar, ku sani an
wuce lokacin bauta. Wadanda kuke bautarwa Allah sai ya
saka musu. Kuma Wallhi sai kun biya su hakkin su a ranar
da baku da komai sai abin da kuka jewa Allah dashi. Ina
rokon wasu daga cikin Directors, Actors, Actresses, writers
da producers.

Mu hadu domin kawo karshen Wannan
zalinci.
Duk wanda aka samu a karbi hakkin wanda yaci kuma a
hukuntashi. Muyi domin Allah bada nufin tozarci ko cin
Zarafin juna ba.

Sai Dan tsaftace Masana'anta daga
hannun baragurbi. Ka fara daga set din da kake. Duk
wanda kaji ba'a biya ba, ka dakatar da aikin har sai an biya
hakkin mutane sannan a cigaba. Domin ni nasan ba'a film
sai da kudi.

The Wallhi duk KABON wanda kaci ka shirya sauraran
hkunci tun daga kabari.
Allah ka tsaremu da zalinci da cin dukiyar wadanda suka
wahaltamana. Ameen.
#gyaran_karaya_movement ".

Inda daga nan kuma shima Ali Nuhu ya fito yayi kira ga
masoyansa da kar su kara cewa komai, koda kuwa an
zageshi suyi shiru dan shi baya zagi ko batancin ga abokin
sana'arsa.
Yanzu dai zamu iya cewa al'amurra sun qazance a
kannywood wanda idan ba'a samu gyara da zaman lafiya ba
za'a koma gidan jiya.

No comments:

Post a Comment