Wednesday, February 14, 2018

[KANNYWOOD] TIJJANI ASASE YAYI GODIYA MAI TARIN YAWA GA MASOYAN SA GA KAUNAR DA SUKA GWADA MASA AKAN ANNOBAR DA TA FADA MASAShahrarren jarumin wasan kwaikwayo na Kannywood,

Tijjani Asase, ya mika sakon nuna godiyarsa ga yan’uwa da
abokan arziki da suka taimaka masa da kayan agaji bayan
annobar gobara ta shafi gidansa.

Zaku tuna cewa a daren Asabar, 3 ga watan fabrairu, 2017
ne annobar gobara ta fada gidansa inda yayi asaran dukkan
dukiyoyinsa ba tare tsirata da komai ba.

Jarumin ya yi wannan sanarwar mika godiya ne a shafin
sada ra’ayi da zumuntarsa kuma jiga-jigai da masu ruwa da
tsaki a masana’antar Kannywood sun kai masa ziyara.

A yayin wannan ziyara da suka kai, wasu daga cikin su sun
agaza masa da kayan abinci da kudi har da sutura.

Yace:"Salam barkanmu da safiya da mika godiyata ga
iyayan gidana da yayyena wa'yan da suka tayani da alhini.

wasu a waya wasu hargida wasa harda gudun mawa sutura
da abinci wasu harda kudi nagode Allah yabar zumunci amin
nagode". ya rubuta a shafin sa na instagram.

No comments:

Post a Comment